Sheikh Ibrahim Sabi'u ya yi kira ga 'yan Social Media da su dinga tabbatar da Ingancin labari kafin su yada shi. Mataimakin shugaban majalissar ta kungiyar JIBWIS dake tarayyar najeriya Sheikh (Barr) Ibrahim Sabi'u Jibia, a yayin da yake gabatar da khudbar sallar juma'a yayi kira ga masu amfani da kafafen sadarwar zamani (Social Media) su guji yada sharri da labarin karya. Ya kara da cewa: yana da kyau mutane su dinga bincike domin tabbar da ingancin labari kafin su yada shi don gudun aikata abinda zai sa mutum ya wayi gari yana mai ladama game da abinda ya aikata. Kazalika ya karanto ayoyi daga alqur'ani mai girma da hadisan Annabi (S.A.W) wadanda suke magana akan haramcin yin irin wannan mummunan aiki, wanda yin haka babban abin kyama ne a wajen Allah madaukakin sarki. A cewarsa tsawon lokaci da ya gabata akan samu batagarin malamai ne masu karantar da hadisan karya a yayin da suke karantar da dalibansu, amma yanzu zamani ya canza, kana kwance a gida za kai ta ...
Yau Lahadi 05/07/2020 Sheikh Barr. Ibrahim Sabiu ya yi shekara daya a matsayin "Sarkin Malaman Jibia". Tarihi ya nuna cewa tun farkon kafuwar masarautar Jibiya ba'a taba bada mukamin Sarkin Malamai ba sai a shekarar data gabata, inda aka dauko daya daga cikin Malaman da ke fadi tashi don ganin addinin Muslunci ya samu gindin zama a fadin duniyar nan. A shekarar data gabata ne, Mai girma Sarkin Arewan Katsina-Hakimin Jibia Alhaji Rabe Rabi'u Ibrahim, ya bada wannan mukami ga Malam Ibrahim Sabi'u, wanda akayi bikin nadin sarautar a ranar juma'a 05/07/2019 da misalin karfe 10 na safe, a fadar mai masarautar dake Jibiya. Barrister Ibrahim Sabi'u, ya kasance dan uwa na jini ga Sarkin Arewan Katsina-Hakimin Jibia Alhaji Rabe Rabi'u Ibrahim, wannan alaka ta nuna cewa 'ya'yan wa da kanine, Sarkin Malamai yaya ne ga Hakimin na Jibiya. An nada Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u a matsayin Sarkin Malamai ne biyo bayan kasancew...